Pakistan ta sha alwashin za ta yi kokarin kyautata dangataka tsakaninta da Amurka, a tattaunawar da za su yi, duk da rashin jituwar da ta biyo bayan wata tattaunawar wayar talho da ta wakana tsakanin sabon Firai Minista Imran Khan da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo.
Yayin wani jawabi da ya yi a zauren majalisar Dattawan, Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mehmood Qureshi, ya musanta cewa an yi wata tattaunawa da ta shafi tsagerun da ke kasar ta Pakistan, a lokacin da Pompeo ya kira Khan ta wayar talho.
Khan ya fadawa majalisar dattawan cewa, babu kanshin gaskiya kan yadda hukumomin Washington suka ba da labarin, dangane da ganawar ta wayar talho wacce aka yi a ranar Alhamis.
Bayanan da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta nada daga tattaunawa, sun nuna cewa, Pompeo ya yi wa Khan fatan samun nasara a yakin da yake yi da ‘yan ta’adda tare da yin kira a gareshi da ya dauki tsauraran matakai akan ‘yan ta’addan da ke kasar ta Pakistan.
Facebook Forum