Shin Matasan Da Aka Kashe A Abuja 'Yan Boko Haram Ne?

The dead bodies of four suspected Boko Haram members in a Civil Defense pickup van, Abuja, September 20, 2013.

Ko dayake jami’ai basu ambaci cewa wadanda suka kashe ‘yan boko haram bane, amma sunce masu aikata ayyukan ta’addanci ne.
Jami’ar labaru ta hukumar ‘yan Sandan Sirri na SSS, wadanda suka harbe matasan, Marylin Orga, tace matasan na aikata ayyukan ta’addanci ne, kuma sunce sun birne makamai ne a gidan. Ta kara da cewa da isar jami’an, matasan sun bude wa jami’ai wuta, su ko suka mayar da martani.

Bayan wadanda suka kashe a gidan, SSS din sun kama wasu mutane da suke tuhuma su 12, dake basu bayanai masu muhimmanci.

Jami’an sun gabatar da wasu matasa biyu, wadanda suka ce su suka fara kamawa, kuma har suka kaisu inda suke taro a gidan, wanda ba’a kamalla gininsa ba, kuma yana unguwar Appo, gab da wani tsauni mai tarihi a kabilar Gwari.

Kamal Abdullahi yace “Ina cikin Masallaci ina Sallah aka kama ni. Ana zargin mu da boko haram.”
Nasiru Adamu El-hikaya ya tambaye shi “shin kai dan Boko Haram ne?”.

Sai Kamal yace “Ina tare da su, kuma wanda yake tare da su, it means, yana cikinsu.”

Abdullahi Abdulmajid, shine shugaban Kungiyar Matasan Najeriya wanda ya garzaya domin gani da idanunsa abunda ya faru.

“Zargansu akayi, saboda doka dai, hurumin da ta bada ga jami’an tsaro, shine kama duk wanda ake zarginsa da yin wani abu da zai kawo matsala a kasa, a kuma kaishi inda za’a zauna, a yi bincike iya gwargwado domin gano bakin zare.” A cewar Abdullahi Abdulmajid.

Babu ko daya daga jami’an SS din da ya ji rauni, inda suke ta kai-kawo, fuskokinsu a rufe da bakaken mayafai, rike da manya-manyan bindigogi.

Mazauna wannan unguwa na tababar cewa matasan ‘yan Boko Haram ne, ko kuwa tsau-tsayi ne ya rutsa da su.

Your browser doesn’t support HTML5

SSS A Najeriya Sun Kashe Matasa Ba Tare Da Hukunci Ba