Wannan ikirari na rundunar sojojin Najeriya na farmakin da suka kai kan sansanin Boko Haram tun ranar 12 ga watan nan na Satumba, yana zuwa ne a bayan da kafofin yada labarai na cikin gida a Najeriya suka ce mayakan Boko Haram sun yi kwanton-bauna suka far ma sojoji a wannan yanki, inda suka kashe guda 40 daga cikinsu, wasu da yawa kuma ba a san inda suke ba.
Jami’an soja da aka tuntuba sun ki cewa uffan a game da kwanton-baunar da aka ce ‘yan Boko Haram sun yi ma sojoji, sai suka gwammace yin magana kawai a kan farmakin da suka ce sun kai kan wannan sansani. A da dai, sojojin ba su bayyana labarin wannan farmakin ba.
Wannan daji na Kasiya inda aka ce an samu sansanin na ‘yan Boko Haram, aka kuma kai masa farmaki, yana da tazarar kilomita 70 a arewa maso gabas da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, kuma cibiyar kungiyar.
Wannan daji da hanyoyin da suke bi ta kusa da shi sun yi kaurin suna cikin ‘yan watannin nan a saboda yadda ake tare mutane ana yi musu fashi.
Akwai rade-radin da ake ji cikin ‘yan kwanakin nan cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sake tattaruwa a wannan daji cikin ‘yan watannin nan.