Bayyanai sun nuna cewa 'yan furzinan sun tada tarzoma ne bayan dan karen dukan da wani cikinsu ya sha sabili da kokarin da ya yi na tserewa daga gidan kason. Shi dan furzunan har ya samu ya hau katangar dake kewaye da gidan kason kafin a hango shi kana aka kama shi aka yi masa duka har sai da ya suma. Daga baya ya mutu domin rashin kula.
Ganin irin dukan da dan furzunan ya sha da kuma rashin kulawa wanda ya kai ga mutuwarsa ya sa furzinonin suka tada tawaye. Kawo yanzu ba'a sani ba ko wasu sun mutu ko sun tsere daga gidan kason. To saidai akwai wanda ya samu rauni. Tuni aka tura sojoji domin tallafawa ma'aikatan gidan yarin.
Masu harsashe suna cewa matsalar cunkoso da rashin wurin kwana mai kyau da rashin abinci da dai makamntansu na cikin dalilan da kan jawo fusatar furzinoni su yi tawaye. Kana gidajen yarin kasar an dade da ginasu. Wasu tun lokacin mulkin mallaka da aka ginasu ba'a sake yi masu wani gyara ba ko ingantasu. Akwai kuma jinkirta hukunci. Wasu suna yin shekara goma ko ma fiye suna jiran hukunci wasu ma bisa ga laifin da bai taka kara ya karya ba.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.