Wadanda aka kashe matsa ne masu sana'ar jigilar fasinjoji da keken nan mai kafa uku da aka fi sani da suna kekenapep. Suna zaune a gidan ne da ba'a gama ginashi ba kuma suna da kungiyar sana'arsu har da katin shaida. Matasan suna biyan maigadain gidan nera dari biyu kowane mako domin su dingi kwana a ciki. Bisa ga bincike mai gidan ya san cewa matasan suna kwana a gidan. Shekaranjiya mai gidan ya basu sati daya su bar gidan. Amma sai jiya da karfe biyun dare ya tattaro jami'an tsaro suka zo suka bude wuta a kan matasan.
A zantawar da wakiliyarmu Madina Dauda ta yi da wadanda ke kwance asibitin Asokoro sun ce jami'an tsaro sun fada cewa wai su 'yan Boko Haram ne shi ya sa suka bude masu wuta. To idan ma 'yan Boko Haram ne me yasa ba'a kamasu ba an gurfanar dasu gaban sharia a hukuntasu? Wani ma da yake ta yin birgima a kasa ya ce kaninsa wanda aurensa saura wata daya na cikin wadanda aka kashe.
Kawo yanzu ba'a san maigidan ba. Wasu sun ce soja ne wasu kuma sun ce wani babban mutum ne. Babu wani jami'in gwamnati ko na 'yansanda da ya san sunan maigidan.Shugabannin matsa da na masu sana'ar kekenapep sun shaida cewa 'yan kungiyarsu ne kuma sana'ar da suke yi.
Gidan a anguwar Apo ya ke kuma duk yawancin gaidajen na 'yan majalisan dokokin Najeriya ne. Su matasan dake gidan da aka hallakasu an ce ba a boye suke ba. An sansu a anguwar. Bugu da kari an nuna katin shaidar wasun su na kungiyar kekenapep.
Ga karin bayani.