Dagacin garin na Tapga, wadda akasarin mazaunanta 'yan kabilar Jukun ne, Mairiga Ubandoma, ya fadawa Muryar Amurka cewa maharan sun lalata gidaje kimanin 100, amma babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskata yawan barnar.
Malam Mairiga Ubandoma yayi zargin cewa 'yan kabilar Tarok ne daga Jihar Filato suka kawo musu farmaki, kuma har ma maharan sun yi ta fadin cewa sun biyo sawun wasu Fulani ne. Da ma dai an samu rikice-rikice a baya a tsakanin Jukun na Taraba da Tarok na Filato.
Wani basaraken kabilar Tarok din ya musanta wannan zargin, yana mai cewa su ma kansu su na fuskantar farmaki ne daga yankin karamar hukumar Langtang a Jiharsu ta Filato.
'Yan sanda sun tabbatar da abkuwar wannan farmakin na Tapga, sun kuma yi kira ga jama'a da su guji daukar doka a hannunsu. Kakakin 'yan sandan jihar Taraba, DSP Joseph Kwaje, yace zasu sanya kafar wando guda da duk wanda ya nemi tayar da fitina.
Shugaban majalisar karamar hukumar Ibbi a Jihar Taraba, Isiyaku Adamu, yace yanzu dai kura ta lafa, kuma har sun rarraba kayan agaji na abinci ga mutanen da suka yi gudun hijira a sanadin wannan farmakin.