A cewar mataikamkin kwamandan Hisba Mallam Yakubu Mai Gida Kachako, ana tuhumar musulman da aka kama basa yin azumi da laifin nuna rashin tarbiya da da’a a cikin bainar jama’a. inda ya kara da cewa zaman marasa azumi akwai barazana ga harkar tsaro domin an kafa hukumar Hisba ne kan doka don haka take amfani da dokar wajen aiwatar da ayyukan hukumar.
Sai dai Barista Audu Bulama Malami dake koyar da darussan laifukan shari’ar shari’ar musulunci a tsangayar nazarin shari’a ta jami’ar Bayero, yace Najeriya kasace dake aiki akan dokoki kuma ita kanta hukumar Hisba doka ce ta kafata, haka zalika babu inda a doka ta mayar da rashin yin azumi laifi ko kuma ta baiwa Hisba damar kama wanda baiyi azumi ba.
Duk da yake rashin yin azumi ga musulmi zunubi ne, amma doka bata ganinsa a matsayin laifi kuma ba ta baiwa hukumar Hisba damar kama wanda baiyi azumi ba.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5