Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Bauchi Na Neman Gafara Daga Ma’aikatanta


Gwamnan jihar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar, ya roki gafaran ma'aikatan jihar har ma da wasu rukunin mutanen da suke karbar albashi daga gwamnatin jihar saboda halin kunci da suka shiga a sanadiyar aikin tantance ma'aikata da aka gudanar a jihar.

Gwamanan ya nemi wannan gafararce a taron manema labarai daya gudanar a gidan gwamnatin jihar, inda yace an tabka kura kuran da suka hada da na gangan dakuma na ajizanci.

Duk da yake mutane sun sha wahala a wannan aiki da akayi na tantacewa, gwamnan ya nemi duk mutanen da suka sami kansu cikin wannan hali da su gafarci gwamnatin jiha. Yin hakan kuwa yasa an gano ma’aikatan bogi masu yawa a bangaren jiha da kananan hukumomi.

Jihar Bauchi dai tace zata ci gaba da tantance ma’aikatanta har sai an samar da wata hanyar amfani da na’urar kwamfuta da zata saukaka wannan aiki.

Saurari cikakkiyar hira da Gwamnan jihar Bauchi Barister Muhammed Abudllahi Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG