Hukumar hada hadar kasuwanci ta jiragen ruwa ko Nigerian Shippers' Council ta bullo da shirin bude sashen a yanar gizo.
Ta yin anfani da sashen dan kasuwa ka iya korafi ko kuma bada labarin wata badakala da ya hanga. Nan da nan take hukumar da wasu hukumomi dake yaki da cin hanci da rashawa zasu samu sakon ta akwatin yanar gizo da ta hanyar wayar salula.
Kwana kwanan nan Shugaba Buhari ya kirkiro da wata cibiya ta shugaban kasa da zata dinga kula da harkokin kasuwanci yadda ya dace domin bunkasa tattalin arziki ta hanyar fitar da kaya waje da kuma shigo dasu Najeriya.
Yayinda yake kaddamar da sashen na yanar gizo mataimakin shugaban Najeriya Farfasa Osinbajo yace lokaci ya yi da jihohi da kananan hukumomi zasu rage dogaro ga rabon kudi daga gwamnatin tarayya su fuskanci hanyoyin samun kudaden shiga a jihohinsu.
Barrister Hassan Bello shugaban hukumar hada hadar kasuwanci ta teku yace sun sa sashensu a yanar gizo kuma kowa yana da 'yancin mika kara ko bada jawabi da zai taimaka ya yi bayanai.
Akan bada tabbacin za'a saurari korafi ko bayani, Barrister Bello yace tabbas zasu dauki mataki akan kowane korafi ko bayani domin aikinsu ke nan. Yace hukumarsa tana kan cewa dole sai an inganta tattalin arzikin kasar kan hanyar sufuri. Kasuwanci ta hanyar sufuri ma zasu ba kasar kudaden shiga fiye da mai.
Barrister Hassan yace shirin da suka fara da can yana nan. Sun bude tasoshi a Funtua, Isialangwa, Kano, Jos, Maiduguri da Ibadan. Yanzu ba sai mutum ya nufi Legas daukan kaya ba. Shirin zai kawo kayan wadannan tasoshin 'yan kasuwa su dauki abunsu. Haka ma idan mutum zai fitar da kaya waje sai ya kai tasoshin su fitar dasu.
Mahalarta taron da suka hada da 'yan kasuwa sun nuna farin cikinsu musamman wadanda suke garuruwan da basa bakin teku. Ahmed Rabiu shugaban tashar kamfanin sauke kaya ta Dala Kano yace suna anfani da kwamfuta ce wadda mutum zai bude ya buga duk abun da yake son ya yi kara akai. Yana gamawa kuma za'a ga korafin a wurare uku. Har majalisar tarayyar Najeriya karar na iya zuwa.
Ga karin bayani.