Shin Ina Manufar Kwamitin da Jonathan Ya Kafa

Zanga-zangar neman a je a kubuto da dalibai mata na Cibok da 'yan Boko Haram suka sace

Makonni uku bayan da aka sace yara mata daga Cibok yanzu gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai binciko wasu dalilai kana ya bada shawarar yadda za'a kubuto da daliban.
Biyo bayan sace yara mata da aka yi ya sa gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti akan yadda za'a samu nasarar samo yaran.

Kwamitin zai duba abubuwan da suka hada da dalilin da ya sa yaran suke makaranta a lokacin bayan sauran yaran suna gidajensu suna hutu. Kwamitin zai binciko su wanene yaran da ainihin adadainsu. Kana ya binciko nawa ne daga cikinsu suka dawo. Kwamitin da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno zai bada shawarar yadda za'a kubuto yaran.

Bayan kwanakin da suka riga suka kwashe a dajin Sambisa a hannun Boko Haram yanzu ba'a san sauran kwanakin da zasu yi ba kafin a kubuto su.

'Yan Najeriya musamman iyayen yaran babu yadda zasu ce gwamnati ta dauki kubuto yaran da mahimmanci kuma cikin gaggawa idan an yi la'akari da cewa a cikin jihar dake karkashin dokar ta baci aka sacesu. Bugu da kari shugaban kungiyar Boko Haram ya fito karara yace su ne suka sace yaran. Domin haka ayar tambaya a nan ita ce ina manufar kwamitin da shugaba Jonathan ya kafa.

Tsohon kwamishanan 'yan sandan jihar Legas Abubakar Tsav yace komi sai shugaban kasa ya kafa kwamiti. Yaran nan sati uku ke nan da aka sacesu kuma babu komi da shugaban yayi. Yace kafa kwamitin ma sabili da matan Cibok da suka yi zanga-zanga ne.A karshe kwamitin ba zai yi komi ba.

Wasu ma sun ce ina tasirin kwamitin da zai yi zamansa a Abuja bayan lamarin ya faru ne a jihar Borno.

Kawo yanzu mata a birane daban daban sun fara shiga zanga-zanga suna kalubalantar shugaba Jonathan da ya hanzarta kubuto yaran. Matan sun ce muddin gwamnati bata kubuto yaran ba nan da dan wani lokaci to su zasu nufi dajin Sambisa. Cikin biyu a yi daya. Ko a dawo da yaran ko kuma su ma a hada da su

Amma Dr Abubakar Sadiq ya kalubali gwamnati. Yace abun da ya faru ya nuna karara gazawar gwamnati. Yace a tuna shugaban kasa ya kwace duk kafofin tsaro. Duka suna hannunsa. Babu kodaya a hannun gwamnonin jihohi. Sabili da haka kwamitin da ya kafa bashi da ma'ana ko wani anfani kuma ba zai yi tasiri ba.

Ga rahoton Ladan Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Ina Manufar Kwamitin da Jonathan Ya Kafa - 3'56"