Shari'ar Oscar Pistorius ta Canja Zane

A watan Oktobar da ya gabata ne aka saki Oscar Pistorius daga gidan kaso, bayan da ya yi kasa da shekara daya a tsare bisa hukuncin daurin shekara biyar da ka yi masa.

Kotun Daukaka Karraraki ta Afrika ta Kudu ta ce ta sami hamshakin dan gudun fanfalakin nan mai nakassar kafafu na kasar, Oscar Pistorius da laifin kisan kai na ganganci, wanna na nufin cewa kotun ta chanja hukuncin da aka yanke mishi a can baya na laifin yin kisan kai ba da niya ba.

A yau ne Kotun Daukaka Kararakin ta bayyana wannan sabon hukuncin da ya chanja wanda aka yanke ma shi bara dangane da kisan buduruwar sa, Reeva Steenkamp.

Alkalin kotu Eric Leach yace ko da Pistorius ya dauka wanda ya auna yana harbi wani da bai sani bane, ko ma kuma ya san cewa buduruwar tasa ce, ya san abinda ya aikata ba daidai bane kuma abin zai iya kai ga asarar ran Bil Adama, saboda haka, a cewar alkalin “ba wani tasiri akan wanda aka kashen, cewa wanda aka sani ne ko wanda ba’a sani ba.”

Da yake laifin kisan kai na ganganci na dauke da hukuncin daurin shekaru akalla 15, yanzu za’a sake maida maganar a kotun farko don sake yanke wa Pistorius wani sabon hukunci.