Ma’aikatar shari’a ta kasar Switzerland ta bada sanarwar cewa an cafke mataimaka biyu na shugaban FIFA da suka hada da Alfredo Hawit da Juan Angel Napout, a cigaba da ake na farautar masu hannu a cikin badakalar cin hanci da rashawa dake addabar hukumar ta kwallon kafa ta duniya.
Ma’aikatar shari’ar ta ce jami’an biyu sun so su yi jayayya da kokarin da aka yi na maido su Amurka don yi musu shara’a. Jami’an na Switzerland sun ce Amurka na tuhumar cewa wadanan jami’an biyu na FIFA sun karbi cin hanci na miliyoyin daloli.
Hewit shine shugaban hukumar da ke kula da kwalon kafa ta Amirka ta Arewa, Amirka ta tsakiya da da yankin tsibirin karebiya. Napout kuma shine shugaban hukumar da ke kula da kwallon kafa ta Amirka ta Kudu.
Mr. Napout da Mr. Hawit dai na cikin jerin jiga-jiggan FIFA da Amurka ta jima tana farauta a sanadin gagarumin almubazzarancin da aka yi a cikin Hukumar FIFA.
Hukumar shari'ar Amirka ta ce tana da damar yin irin wannan kamen saboda jami'an na hukumar FIFA sun yi amfani da bankunan Amirka wajen gudanar da harkokinsu.