A wajen wani wurin shakatawa da ‘yan yawon bude ido ke zuwa da ake kira Waza ne aka kai harin, inda mutane takwas suka mutu ciki harda maharan biyu da suka tarwatsa kansu, sai kuma wani da sojojin Kamaru suka kashe kafin ya sami nasarar tada bom din da ke jikinsa, a cewar Gwamnan jihar ta Arewa mai nisa Malam Mijin Yawa Bakari, a lokacin da ya yi wa manema labarai jawabi a ofishinsa.
Ministan Labarai, kakakin gwamnatin kasar Kamaru kuma, Isah Chiroma Bakari, ya ce yanzu haka dai kasar Kamaru ta chafke shugaban ‘yan Boko haram na kasar mai suna Abba Gana, wanda ke jagorantar hare-haren da ake kai wa a fadin kasar baki daya. Kuma ya ce dakarun tsaron Kamaru da na Najeriya na aiki kafada da kafada tsakaninsu don murkushe ‘yan boko haram.
Isah Chiroma ya kuma ce lamarin ‘yan boko haram ya kusan zama tarihi a kan iyakokin kasashen guda biyu.
An kuma gano gawarwakin wasu mutane guda bakwai a gonar wani dan Najeriya amma mazaunin wani Kauye a jihar Littoral kuma yanzu haka suna hannun ‘yansandan kwana-kwana don yin binciken kwakkwab, Akan haka ne gwamnan jihar ta Littoral, Dieudonné Ivaha Diboua ya kai ziyarar gani da ido wurin. Gwamnan ya ce mutumin dai a halin yanzu ya tsere amma jami’an tsaro na cigaba da bincike don gano gaskiyar lamarin.
Ga karin bayani daga Muhamman Awal Garba.