Ma'aikatar shari’a ta Amurka tace zata dauki matakin na ba safam ba, kamar yadda Atoni janar kuma ministan shari’a na kasar Jeff Session ya fada, na neman kotun koli ta tayi watsi da hukuncin da wata kotu a jahar California ta zartas na hana gwamnatin tarayya daina aiki da shirin kare wadansu da aka kawo Amurka tun suna yara daga maida su kasashen su.
Gwamnatin Trump ta fada jiya Alhamis cewa zata shigar da bayanai gaban kotun kolin domin ta sake duba hukuncin da ta yanke a California. Matakin ba safai ake haka ba,domin gwamnatin ta dauki matakin ne gabannin a gama sauraron daukaka kara da ahalin yanzu yake gudana a gaban kotun daukaka kara dake San Francisco.
Atoni Janar Session yace hukuncin da alkalin ya yanke “ya kaucewa doka da duk wani tunai” ace alkali daya rak zai yanke hukunci kan makomar shirin da ake kira DACA, matakin da zai shafi dukkanin kasar.
Atoni Janar na jahar California Xavier Becerra ya maida martani kan matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka da cewa, ya hakikance alkalan manyan kotunan kasar za su fahimci dalilin d a yasa alkalin kotun kasa, ya bada umarnin ci gaba da aiki da shirin har sai an kammala kararraki da aka shigar gaban kotun dagane da btun.
Tunda farko, a wunin jiya sai da shugaba Trump ya soki ‘yan Democrat inda yake cewa suna shirin jawo tsaiko ga harkokin gwamnatin daga karshen wannan mako, saboda kawai su kare wadanda shirin na DACA ya kare, matakin da yace zai hana dakarun Amurka samun kudaden tafiyar da ayyukans su.