Rahotanni daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na cewa 'yan sa kai na maharba da 'yan banga sun sami nasarar kashe wasu daga cikin 'yan Boko Haram da suka kai hari Pallam dake yankin Madagali a jiya Talata.
To sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da al’ummomin yankin ke yin kuka game da sabbin hare-haren da ake samu a yankin cikin kwanakin nan.
Yanzu haka, ana yawaitar samun harin sari ka noke da ake zargin mayakan Boko Haram na kaiwa a wasu wuraren da aka kwato a yankunan Madagali da Michika cikin 'yan kwanakin nan, lamarin da ke kara tada hankulan al’ummomin da suka koma.
Na baya bayan nan shi ne harin da suka kai garin Pallam dake Madagali inda aka samu asarar rayuka, koda yake daga bisani 'yan sa kai na maharba sun yi musu kwanton-bauna,inda aka kashe wasu daga cikin 'yan Boko Haram,kamar yadda wani dan yankin ke cewa.
To sai dai kuma, wata matsalar da jama’ar yankin ke kokawa a kai ita ce ta rashin kai musu dauki cikin gaggawa daga jami’an tsaro.
To wai ko me jami’an tsaron ke cewa ne game da wannan zargi na nokewa? SP Othman Abubakar, kakakin rundunan 'yan sandan jihar Adamawa, yace ba haka zancen yake ba. Yace matsalar rashin isassun jami’ai na zama kandagarki na kaiwa ga irin wuraren da ake kai harin ba wai nokewa ake yi ba.
Mr Adamu Kamale, dan majalisar wakilai ne dake wakiltar wannan yankin da ake yawaitar kai hare haren. Yace su bukatarsu ma ita ce shugaban kasa Buhari ya ziyarce su don gane wa idanuwansa halin da suke ciki.
Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Facebook Forum