Al’umman Fulanin dake Katibu, Baba Gasa, da kuma Donada wadanda aka kaiwa hari da kona musu gidaje a yan kwanakin nan, sun bayyana jin takaicinsu, yayinda suke zargin gwamnatin jihar Taraba da rashin jajantawa ko kuma basu kayakin tallafi, kamar yadda aka baiwa wasu da tashin hankalin na karamar hukumar Lau ya shafa.
Muhammad Modibbo Ali, daya daga cikin wadanda suka rasa yan’uwansu a wannan tashin hankalin, yace kawo yanzu ko kwandala gwamnatin jihar bata basu ba, domin haka ya bukaci gwamnatin jihar da ta duba lamarin da idon rahama.
Shima da yake karin haske, wani mazaunin yankin, Mallam Bello Babni Ja’e yace kawo yanzu kusan mutunen da wannan tashin hankali ya shafa suna cikin halin ban tausayi.
To sai dai kuma a martanin da gwamnan jihar Taraban, Darisu Dickson Isiyaku ya maida ta bakin hadiminsa ta fuskar harkokin yada labarai Mr Bala Dan Abu, ya musanta zargin cewa basu da labarin inda aka tsugunar da ‘yan gudun hijira.
A nata bangaren rundunan yan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta ASP David Misal tace ta na kokari wajen wanzar da zaman lafiya a wannan yakin, inda yace yanzu burinsu shine hana sake faruwar irin wannan tashin hankali, ya kuma bayyana cewa, kawo yanzu babu wanda aka kama.
Ga dai rahoton da wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya aiko:
Facebook Forum