Tun bayan barkewar yakin, rundunar sojin Rasha take kai hare-hare akan wuraren taruwar jama'a irinsu kasuwanni da gidajen zama da kayayyakin more rayuwar farar hula irinsu makarantu da asibitoci.
"A duk shekara, a kowane wata, a kowane lokaci na hunturu, Shugaba Putin na kokarin yin amfani da sanyi a matsayin makami domin tilasta dimbin farar hula barin gidajensu zuwa makwabtan kasashe," a cewar jami'ar gudanarwa a hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID), Samantha Power.
"Don haka, a yayin da muke shirin shiga hunturu, yana sake fatan yanayi zai bashi karin dama, da kuma fatan al'ummar Ukraine da saurnmu zasu gaji a kan tafarkin da muke kai. Ina tunanin mun taru ne a yau domin karyata wannan fata na shi-kuma cacar daya dauko ba mai cin ba ce, kuma dama can hakan take har zuwa yanzu."
A ranar 23 ga watan Satumbar daya gabata, kungiyar kawancen siyasa da tattalin arzikin kasashe ta G-7 data kunshi kasashen Kanada da Faransa da jamus da Italiya da Japan da burtaniya da Amurka da kuma tarayyar Turai sun gana a gefen taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na 79 domin tattaunawa akan matakan daya kamata a dauka domin tabbatar da cewa shirin Putin na yin amfani da yanayin hunturu wajen azabtar da al'ummar Ukraine bai yi nasara ba.
Tun cikin hunturun 2022, kasashen G-7 suka tara fiye da dala biliyan 4. A yayin da Amurka ta bada fiye da dala bilyan 1.8 tun a watan Febrairun 2022," a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken. "Hakan ya zamo dalili na zahiri da zai sa mu taimakawa abokanmu na Ukraine wuce wadannan watanni lafiya, musamman tsallake yanayin hunturu."
"Mun sake hakikancewa cewar ba hasashe bane, zahiri ne cewar Putin zai yi amfani da hunturu a matsayin makami, mayar da yanayi makami, zai yi amfani da makamashi a matsayin makami a kokarinsa na mamaye kasar Ukraine.
Kuma mun san cewar hunturu mai kamawa sai kasance da kalubale, wannan shine dalilin daya sanya kasashenmu ke aiki tare a kowace rana wajen tabbatar da cewa Ukraine ta samu dukkanin abinda take bukata domin wuce hunturu lafiya."
A cewar Blinken, "babbar manufarmu anan ita ce, kowace kasa daga halartar wannan taro-dama wasu da dama - na goyon bayan kasar Ukraine bil hakki. Mun kudiri aniyar ganin Ukraine tayi nasara. A shirye muke mu cigaba da taimakawa al'ummarta a yayin da suke fuskantar wannan yaki.
Wannan Sharhi Ne Dake Fadin Ra'ayin Gwamnatin Amurka.