Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Hamas Ba Ta Da Gurbi A Makomar Gaza


Anthony Blinken
Anthony Blinken

A jawabin da ya gabatar a wurin taron tsaro na ASPEN, akan yiwuwar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya ce: “nayi imani cewa mun dau hanyar da zai kai ga cimma manufar tsagaita bude wuta, a sako mutanen da ake garkuwa da su."

Ya kuma ce sannan ta dora mu akan hanya madidaiciya wacce zata kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa da tabbatar da tsaro. Abin da ya rage ayi yanzu shine, a kammala wasu abubuwa masu mahimmanci ga wannan tattaunawar sulhun.”

A bangaren tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da tsaro a dogon zango kuma, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Mathew Miller ya ki ya ce uffan a game da yiwuwar ko akwai wata rawar da Hamas zata taka a harkokin tafi da al’amuran gwamnatin Gaza.

Yayi Magana ne bayan jawaben bangarorin Hamas daban-daban cikin su har da Hamas da Fatah wadanda suke tafi da al’amuran hukumomin Faladsinawa, wadanda suka rattaba hannu a wata yarjejeniya karkashin jagorancin China wanda zai kai ga samar da kafa gwamnatin hadin kai bayan yakin Gaza.

“Idan muna Magana a game da harkokin tafi da al’amuran gwamnati a Gaza bayan rikicin, babu kungiyar ta’addancin da za abata damar aiki a gwamanti. Tunb a yau ba Hamas ta kasance kungiyar ta’addanci. Alhakin fararen hular da basu jib a basu gani ba yana wuyar su. Kamar yadda muka sanar, nuna fata mu ga cewa hukumomin gwamnatin Falasdinu sun yi aiki don samun hadin Gaza da gabar tekun maliya.”

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Miller, ya ce Amurka ta karfafawa China gwiwa don ta yi amfani da karfin fada ajin da take da shi a kasashen yankin wadanda take hulda da su wajen ganin ba a sake dago wannan rikicin ba.

“Misali, Iran wacce ta ci gaba da tallafawa kasashen da ke kawance da Filasdinu da kaiwa Isra’ila hare-hare musamman ma kungiyar Houthi wace ta kaddamar da hare-hare akan jiragen dakon kaya na ‘yan kasuwa, mun bukaci China ta yi amfani da tasirin ta wajen kokarin ganin ta kawo karshen wadannan hare-haren sannan zamu ci gaba da tuntuba.”

Khakaki Miller, ya ayyana cewa, duk da yarjejeniyyar hadin kan da kuma jawaben da mai Magana da yawun Hamas yake gabatarwa daga lokaci zuwa lokaci, Hamas a matsayin ta na kungiya, bata fito fili ta bayyana matsayar ta akan daina tashin hankaliba, ci gaba da goyon bayan ayyukan ta’addanci, ko kuma goyon bayan ta ga durkusar da kasar Isra’ila ba.”

“A karshe, mai Magana da yawun hukumar Miller, ya ce hanyar da ta fi dacewa don tabbatar da cewa Hamas bata sake karfafa kanta basannan ta tabbatar da matsayin ta a cikin Gaza ba, shi ne a samarwa al’ummar Falasdinu wata mafita a siyasance. Kuma abin da muka dukufa yi Kenan. Kuma shi ne abn da muka yi ta kokarin cimmawa da sauran wadanda muke aiki tare a yankin.”

Wannan sharhi ne na gwamnatin Amurka

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG