Wata hira ta musamman da wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Nijar game da rashin Zartas da kudurin CEDEAO.
NIAMEY, NIGER - A yayin da aka yi hasashen yiwuwar kungiyar CEDEAO ta zartar da kudirinta na amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar bayan shudewar wa’adin da aka ba su don ganin sun maida Shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa, harakokin yau da kullum sun gudana a birnin Yamai ba tare da wata fargaba ba.
To ko wace irin fassara za a iya yi wa matsayin na ECOWAS? Tambayar da muka yi wa Abdourahamane Alkassoum ke nan wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijar a wata hira tare da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Saurari yadda hirar tasu ta kaya:
Your browser doesn’t support HTML5