Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa'adin ECOWAS: Ana Ci Gaba Da Adawa Da Shirin Tura Dakaru Nijar


Wasu daga cikin hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)
Wasu daga cikin hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)

A ranar Asabar Majalisar Dattawan Najeriya da ke makwabtaka da Nijar, ta ki amincewa da shirin daukan matakin soji da ECOWAS ta yi barazanar yi.

A ranar Lahadin nan, wa’adin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta sakawa dakarun da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar kan su maido da Shugaba Mohamed Bazoum karagar mulki ko a dauki matakin soji akansu ke cika.

Wa’adin na shirin cika ne yayin da ake ta ci gaba da kiraye-kiryan bin wasu hanyoyin na lumana wajen warware rikicin shugabancin kasar.

Dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasa sun tsare tare da ayyana juyin mulki a Nijar a ranar 26 ga watan Yuli.

A ranar Asabar Majalisar Dattawan Najeriya da ke makwabtaka da Nijar, ta ki amincewa da shirin daukan matakin soji da ECOWAS ta yi barazanar yi, inda ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar, da ya duba wasu hanyoyi wajen shawo kan rikicin.

“Ba huruminsa ba ne (Shugaba Tinubu) shi kadai, ba shi da wannan ikon ya shiga yaki da wata kasa ba tare da ya kawo dalilansa a gaban majalisa ba.” In ji Sanata Abdul Ningi.

Kungiyar ECOWAS na da hurumin da za ta yi gaban kanta, idan har mambobinta suka amince da kai harin.

Sai dai gargadin da a ke ta yi daga kasashen yankin kan mummunan tasirin da harin sojan na dasa alamar tambaya kan makomar wa’adin da ECOWAS din ta shata.

Kasashen Aljeriya da Chadi, wadanda ba mambobi ba ne a kungiyar, sun nuna adawarsu da matakin, yayin da Mali da Burkina Faso, wadanda ke karkashin mulkin soji, suka ayyana cewa matakin tamkar kaddamar da yaki ne akansu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG