Shaharraren tsohon dan kwallon kafar kasar Brazil, Pele, ya rasu a yau bayan ya yi fama da jinya.
WASHINGTON, D.C - Pele ya rasu ya na da shekara 82 a dubiya.
Shi ne dan kwallon da yafi kowanne zura kwaalaye a duniya, inda ya ci 1,281 a cikin wasanni 1,363 da ya buga a tsawon shekara 21 da ya yi yana wasa.
An yiwa Pele tiyata inda aka cire mushi wani kulu a cikin hanjinsa a watan Satumban 2021 a wani asibiti a Sao Paulo.
An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022.
Mutane a fadin duniya suna jinjinawa Pele a matsayin daya daga ciki mashahuran ‘yan wasan kwallon kafa na kowanne lokaci.
An haife shi ne a 1940 a Tres Coracoes, wanda ke da nisan kilomita 250 daga arewa maso yammacin birnin Rio de Janeiro, kuma yana dan shekara 15 ya sanya hannun kwantiragi da kulob din Santos.