Ana ganin cewa wani jirgin ruwa ne dauke da mutane sama da 100 ya taso daga kasar Senegal zuwa tsibirin Canary na Spain a ranar 10 ga watan Yuli amma bai kai inda ya ke niyya ba. Fiye da bakin haure 60 ne ake fargabar sun mutu sakamakon hantsarin da suka gamu da shi a balaguron.
A makon da ya gabata ne wani jirgin kamun kifi na kasar Spain ya ceto mutane 38 da aka kawo Cape Verde kafin a mayar da su Senegal.
Jami'an Senegal sun ce wani jirgin soji ya maido da maza 37 da suka hada da kananan yara biyar da wani dan kasar Guinea-Bissau, daga tsibirin Sal Island na Cape Verde a ranar Litinin. 'Yan jaridar Associated Press sun ga wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu an dauke su cikin motocin daukar marasa lafiya a filin jirgin saman Dakar babban birnin Senegal. Mutum daya da ya tsira ya cigaba da kasancewa a asibiti a babban birnin Cape Verde na Praia, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.
Hanyar kaura daga yammacin Afirka zuwa Spain na daya daga cikin hanyoyi mafiya haɗari a duniya, amma duk da haka adadin bakin hauren da ke fitowa daga Senegal a cikin kwale-kwalen katako mara karfi ya karu a cikin shekarar da ta gabata.
A cikin watanni shida na farkon shekarar 2023, kusan mutane 800 ne suka mutu ko kuma su ka bace a tekun Atlantika a kokarinsu na isa tsibirin Canary, a cewar kungiyar kare hakkin Spain ta Walking Borders
Annette Seck, Ministar 'yan kasar Senegal dake zaune a kasashen waje, ta fada a wani taron manema labarai cewa, an binne gawarwakin mutane bakwai da aka gano a cikin kwale-kwalen a wurin a Cape Verde. Ta godewa mahukuntan Cape Verde domin agazawa bakin hauren tare da mika ta'aziyyarta ga iyalan mutanen Senegal din da suka rasa rayukansu.
Masunta da manoma a Fass Boye sun dora alhakin kasadar da matasa su ke yi su sadaukar da rayukansu ta wajen tfiya cikin kwale-kwale da ya yi mummunan cunkoso kan rashin aikin yi.
A cewar Seck, akalla manyan kwale-kwalen kamun kifi guda 20 da ake kira pirogues cike da bakin haure sun bar garin cikin shekaru ashirin da suka gabata.
~ AP