Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SENEGAL: Akalla Bakin Haure 8 Sun Mutu a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa


Kwale-kwale da ya nutse
Kwale-kwale da ya nutse

An gano gawarwakin bakin haure takwas bayan da wani kwale-kwale ya kife a gabar tekun arewacin kasar Senegal a lokacin da yake kokarin shiga Turai.

Ministan harkokin cikin gida Felix Abdoulaye ya ce jami’an kashe gobara da na ruwa ne suka gano gawarwakin, kuma an kaddamar da aikin neman wadanda suka tsira.

Mourtalla Mbaye, darektan dakin ajiye gawarwaki na Saint-Louis a arewacin birnin kamun kifi na Saint-Louis inda aka kawo gawarwakin, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa kimanin mutane 155 ne ke cikin jirgin.

Wasu bakin haure a jirgin ruwa
Wasu bakin haure a jirgin ruwa

Yawancin wadanda suka tsira sun sami raunuka kuma suna karbar magani a wani yanki na sojoji a birnin. Ya ce gawarwaki shida mutane ne da suka nutse, kuma ba a san adadin mutanen da suka tsira ba kuma har yanzu ba'a gansu ba.

Wasu bakin haure da aka ceto
Wasu bakin haure da aka ceto

Kwale-kwalen da aka ceto da yammacin jiya Laraba, ya zo ne kwanaki bayan da aka samu gawarwakin wasu bakwai da kuma ceto 50 a wani jirgin ruwa na daban wanda shi ma ya nufi Turai da aka gano a gabar tekun Saint-Louis.

Akalla mutane 90 ne ake fargabar bacewarsu daga wannan jirgin

~AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG