WASHINGTON, D.C. - Lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 79 tare da bacewar wasu da dama a cikin wani bala’i mafi muni da ba taba gani ba a wannan shekarar.
Jami'an tsaron bakin teku, jiragen ruwa da na 'yan kasuwa da jiragen sama sun fito gadan-gadan domin gudanar da wani gagarumin aikin bincike da ceto wanda zai ci gaba har cikin dare.
Ba a dai san iya adadin fasinjojin da suka bace ba, amma wasu rahotannin farko sun nuna cewa watakila daruruwan mutane ne a ciki lokacin da kwale-kwalen ya gangara nesa daga gabar teku.
Firai Ministan rikon kwarya na Girka, Ioannis Sarmas, ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa, ya kuma ce "tunaninmu na tare da ku duk wadanda suka mutu a cikin wannan mummunan lamarin na ‘yan fasa-kwauri da ke cin gajiyar jin dadin bil'adama.
Kakakin hukumar tsaron gabar tekun, Nikos Alexiou ya shaidawa gidan talabijin na ERT na jihar cewa ba zai yi wu a iya tantance cikakken adadin fasinjojin ba.
Ya kara da cewa, bisa ga dukkan alamu jirgin mai tsawon mita 25 zuwa 30 (kafa 80 zuwa 100) ya kife ne bayan da mutane suka koma gefe guda ba zato ba tsammani.
"Babban bene na cike ne da mutane, kuma muna tsammanin cewa tsakiyar (na jirgin) ma ya cika," in ji shi.
"Da alama akwai wani canji a cikin motsin mutanen da suke a cunkushe a cikin jirgin, kuma ya kife." Ya kara da cewa.
-AP