Jami’ai sunce ba dan an ‘dauki wannan mataki ba, da an sayar da tulin abincin ne ga mahajjata. Dakta Ibrahim Abubakar Kana, shine jagoran likitocin Najeriya dake kula da lafiyar Alhazai a kasa mai sarki. Yace sunyi na’am da wannan mataki da Saudiyya ta dauka, inda ya kara da cewa akwai mutanen dake daukar abincin da ya gurbata su sayarwa da mutane.
Tun da farko sai da mahukantan Saudiyya suka kwace tare da lalata nau’o’in gurbatattun abinci 140,000 da aka so shiga da su birnin Makka, don sayarwa ga mahajjata. Acewar Imam Abdullahi Bala Lau, dake zaman shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah a Najeriya, wannan mataki shine ma’anar kyakkyawan shugabanci abin koyi.
Kwararre a sha’anin aikin Hajji Mohammed Adam Abubakar, yace shigowa da irin wadannan mummunan abu ga al’umma wani abune da zai cutar da al’umma, don haka abin da sukayi yayi dai dai a tsari na zamantakewa na rayuwar dan Adam.
Saurari cikakken bayani daga Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5