Ministan, Chief Audu Ogbe, ya kaddamar da shirin ne a Birnin Kebbi fadar gwamnatin jihar Kebbi.
Yace duk da korafe korafen da ake yi na tsananin rayuwa gwamnatin Najeriya ba zata ja da baya ba a shirinta na wadatar da kasar da cimaka. Yace gaskiya ne akwai matsalar abinci, yunwa da karancin kudi amma jama'ar birane ne lamarin ya fi shafa ba yankunan karkara ba inda ake noma.
Ba zamu mayar da hanun agogo baya ba a sabon tsarin namu domin ko ya zama wajibi mu noma wa kanmu abinci, inji Chief Ogbe. Yace shigowa da abinci daga kasashen ketare ba mafita ba ne. Yace kasar tana da kasa mai albarka tare da manoman.
Inji Chief Ogbe ragwanci ne ya addabi kasar can baya kuma babu wata hujja da cigaba da ragwancin.
Gwamnan jihar Kebbi yana ganin kwalliya ta soma biyan kudin sabulu.Gwamnan ya ce lallurar da take addabar Najeriya ta faru ne sanadiyar lallulororin dake cikin duniya. Yace an samu canjin kasuwanni daban daban cikin duniya. Baicin hakan ba'a sayen kayan da Najeriya ke sarafawa hatta man fetur..Faduwar farashi da tashin hankali a yankin Niger Delta duk sun taru sun dagula lamura.
Gwamnan ya cigaba da cewa ba domin tsarin da shugaba Buhari ya fito dashi ba da munin tabarbarewar tattalin arziki ya fi haka.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.