Sai dai kuma yayin da ma’aikatan kiwon lafiya suka darawa, sai ga wata sabuwa kunnu, inda kungiyar Malamai NUT ke ikirarin saka kafar wando daya da gwamnatin jihar, inda shugabannin kungiyar malaman ke nuna bacin rai game da abin da suka kira shakulatin bangaro da suke zaigin ana nuna musu game da hakkokinsu da suke bi bashi.
Shugaban kungiyar malaman ta NUT reshen jihar, ya gargadi gwamnatin jihar da cewa sun gaji da alkawari, kuma turi ya zo bango domin ya baiwa gwamntin wa’adin kwanaki bakwai da ta biya ko da watanni biyu ne cikin watanni Hudu, in kuma ba haka ba to babu tabbacin cewa kungiyar ba zatayi tafiyar lafiya ba.
A nasa martanin game da wannan batu na albashi gwamnan jihar Sanata Mohammadu Bindo Umaru Jibrilla, yace gwamnatinsa na kokari, domin sun tarar da bashin watanni biyar da ma’aikata ke bi, amma yanzu haka an biya na watanni uku saura na wata biyu.
Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.