Dubban magoya bayan jam’iyyar MODEN LUMANA sun hallara a kofar cibiyar wannan jam’iyyar domin tarbar shugaban reshen Yamai Sumana Sanda da abokansa biyar, wandanda hukumomin Nijar suka garkame tun ranar 14 ga watan Nuwambar 2015.
A lokacin da yake jawabi Sumana Lumana ya tuna da sauran jiga jigan jam’iyyun adawa kusan 20 da ake ci gaba da tsarewa yanzu haka.
Zaman doya da manya da tsakanin magoya bayan MODEN LUMANA da gwamnatin jamhuriya ta bakwai ya samo asali ne tun bayan da Hamma Amadu da makarrabansa suka ki karbar mukaman da shugaba Isoohu ya basu a gwamnatin da ya kafa a watan Agustan 2013, suna masu cewa fanko ne aka basu, a cigaban wannan takaddama jam’iyyar MODEN LUMANA na zargin masu mulki da bita da kullin siyasa akan ‘ya ‘yan ta, yayin da jam’iyya mai mulki PNDS ke cewa wannan korafi bashi da tushe.
Saurari rahotan Sule Muminu Barma.