Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Illar Da Sare Itatuwa Domin Yin Makamashi Ke Haddasarwa


Rahotanni a Najeriya na nuni da cewar a kowacce rana akan sare itatuwa kimanin Miliyan Daya da Dubu Dari Biyar domin yin makamashi.

Bincike ya nuna cewar talauci da rashin ayyukanyi da ma jahilci na daga cikin dalilan da yasa yawancin yan kasar ke sarewa, domin amfanin girke girke a gidajen dai dai kun jama’a da kuma wuraren sayarda abinci.

Ministar ma’aikatar Muhalli Hajiya Amina Mohammed, ta bayyana halin da dazukan Najeriya ke muskanta da cewa ana sare kashi uku na yawan dazukan anas are itatuwan da suke ciki, inda tace wannan babbar matsalace da za a mayar da hankali akai don shawo kanta.

Masana kan gurbatar muhalli sun alakanta sare itatuwa da jama’a ke yi don makamashi da kuma hanyar dogaro da kai na haddasa illoli masu yawa da suka hada da zaizayar ‘kasa samun karancin ruwa da kuma dumamar yanayi.

Saurari cikakken rahotan Abdulwaba Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG