Saudi Arabiya Zata Dauki Matakan Tabbatar Da Aikin Hajji Cikin Lumana

Mahajjata su na addu'a a Dutsen Arafat lokacin aikin Hajjin bara.

Yarima mai jiran gado, Nayef bin Abdulaziz, ya fada cewa a shirye kasar ta tinkari kowane irin lamari cikin lumana, amma kuma zata yi amfani da dukkan karfinta wajen tunkarar duk masu niyyar tayar da zaune tsaye

Saudi Arabiya ta yi kashedin cewa zata dauki dukkan matakan da suka kamata domin tabbatar da cewa an yi aikin Hajji cikin lumana, yayin da ake fama da yamutsi a wasu kasashen larabawa, tankiya kuma ta ke karuwa tsakanin ita Sa’udiyya da kasar Iran.

Sabon Yarima mai jiran gadon sarautar Sa’udiyya, Nayef bin Abdulaziz, ya ce a shirye kasar ta ke ta tinkari kowane irin lamari cikin lumana, amma kuma zata yi amfani da dukkan karfinta wajen tunkarar duk masu niyyar tayar da zaune tsaye.

Musulmi fiye da miliyan daya da dubu dari biyar ne suka riga suka isa kasar ya zuwa yanzu domin gudanar da aikin Hajjin bana da za a fara ranar Jumma’a. A ranar asabar za a gudanar da hawan Arafat, wanda shi ne aikin ibada mafi muhimmancilokacin aikin Hajjin.

Maniyayyata da yawa sun isa can da wuri domin su samu sukunin ziyarar Masallatai masu Tsarki na Harami a Makka da Masjidil Nabawi dake Madina.

Kasar Sa’udiyya dai ta tsere daga irin zanga-zangar da ta baibaye kasashen larabawa da yawa a wannan shekara, har ta kawo faduwar shugabanni a kasashen Tunisiya da Masar da Libya da kuma yamutsi a Sham da Yemen da kuma Bahrain.