Majalisar dokokin Amurka na yunkurin kara tsaurara matakan ladabtar da Iran bayan bullar labarin watan jiya na cewa Iran ta shirya wata makarkashiyar neman yin kisan gilla ga jakadan Saudiyya dake nan Washington.
A yau Laraba kwamitin majalisar wakilai mai kula da al’amuran kasashen waje ya zartas da wata gagarumar dokar da za ta tsananta takunkumin da Amurka ta zargawa Iran game da hada-hadar kudi da man fetur da kuma nukiliya.
Matakan sun kunshi cewa ba za a bayar da izinin shigowa Amurka ba, wato biza, ga duk wanda ke hulda da masana’antun kasar Iran na man fetur ko kuma iskar gas. Akwai kuma wani gyaran dokar da aka yi da nufin katse hulda tsakanin babban bankin kasar Iran da kasuwannin kudin duniya. Haka kuma dokar za ta yi kokarin mayar da jami’an tsaron kasar Iran saniyar ware sannan kuma ta kara k’aimi ga masu zanga-zangar nuna k’in jinin gwamnatin kasar Iran ta hanyar bunkasa musu dabarun tsara zanga-zanga da kuma hanyoyin sadarwa.
Gwamnatin kasar Iran ta musanta cewa da hannun ta a cikin duk wata makarkashiyar neman yin kashe-kashen gilla a wasu kasashen waje.