Jami’an gwamnatin kasar Saudiyya sun ce Musulmi fiye da miliyan biyu da rabi ne su ka yi Hajin bana. Haji ne aikin Ibada mafi dadewa a duniya kuma mafi tsarkaka a addinin Islama, kuma ya wajabta akan dukkanin Musulmi maza da mata masu hali da kwarin jiki. A Makka aka haifi Annabi Muhammad (SAW).
Dubban daruruwan Musulmi sun yi jifan shedan a yau Lahadi bayan sun yi hawan Arfa a jiya Asabar. Wajibi ne ga kowane alhaji ya jefa duwatsu 21,wato dutse 7-7 a kan kowace jamra daya daga cikin ukkun dake jere a zaman shedan.
Bayan jifan shedan sai alhazai su koma Makka su yi dawafi a Dakin Kaaba, wanda a jikin shi dutsen shan nono (Hajr Aswad) ya ke makale, shima dutsen yana daga cikin abubuwan tarihin Addinin Islama mafiya tsarkaka.
Haka kuma a yau Lahadi ake Eid al-Adha wato Sallar Layya, ta yankan sadaka domin tunawa da lokacin da Annabi Ibrahim (AS) Ya bi umarnin Allah (SWT) Ya kusa yanka dan shi Annabi Ismail (AS).