Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta gabatar da takardun tuhumar wasu ‘yan kasar Iran biyu gaban kotu jiya talata, tana zarginsu da laifin hada baki da wasu a cikin gwamnatin kasar Iran don kulla makarkashiyar kashe jakadan kasar Saudi Arabiya a Amurka, Adel al-Jubair.
Fadar White House ta ce shugaba Barack Obama ya kira jakadan Sa’udiyya domin bayyana bakin cikin wannan makarkashiya da ya ce ta keta dokokin Amurka da na kasashen duniya. Sanarwar ta ce shugaba Obama ya kuduri aniyar kare dukkan jami’an jakadancin dake aiki a Amurka, ya kuma yi nuni da dangantakar kut da kut dake tsakanin Saudi Arabiya da Amurka.
Jami’ai sun ce daya daga cikin Iraniyawan shi ne Manssor Arbabsiar, wanda ke rike da fasfo na Iran da na Amurka, wanda kuma aka kama ranar 29 ga watan Satumba a filin jirgin saman John F. Kennedy dake New York.
Jami’an suka ce mutum na biyu shi ne Gholam Shakuri, dan rundunar dakarun Iran da ake kira Quds wanda kuma ke zaune a can Iran din. Suka ce har yanzu ba a kama Shakuri ba.
Atoni janar na Amurka, Eric Holder ya fadawa taron ‘yan jarida cewa an kitsa, aka tsara aka samar da kudin gudanar da wannan makarkashiya daga cikin kasar Iran. Yace Amurka zata dora ma gwamnatin Iran alhakin wannan lamarin.
A jiya talata, kasar Iran ta bayyana wannan zargi na Amurka a zaman kage.