Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Fiye Da Miliyan Biyu Da Rabi Sun Yi Hawan Arfa


Alhazai na addu'a a Arfa da ke bayan garin Makka mai tsarkaka
Alhazai na addu'a a Arfa da ke bayan garin Makka mai tsarkaka

A Addinin Islama Haji ne aikin Ibada mafi dadewa a duniya kuma mafi tsarkaka

Jami’an gwamnatin kasar Saudiyya sun ce Musulmi masu aikin Haji su fiye da miliyan biyu da rabi na hawan Arfa a yau asabar.

A Addinin Islama Haji ne aikin Ibada mafi dadewa a duniya kuma mafi tsarkaka. Ana gudanar da mafi yawancin aikin na Haji a birnin Makka mai tsarkaka, kuma Mahaifar Annabi Muhammad (SAW).

Yariman Saudiyya mai jiran gado Nayef Bin Abdel Aziz yace a jiya-jiyan nan Jumma’a, Alhazai kimanin miliyan daya da digo 8 ne suka sauka a kasar ta Saudiyya. Ya ce bakin Alhazai da suka je sauke farali sun fito ne daga kasashe 183, wadanda su ka hade da dubban daruruwan Musulmin kasar ta Saudiyya wadanda su ma suke yin aikin Haji.

Yeriman Saudiyya mai jiran gado Nayef bin Abdelaziz
Yeriman Saudiyya mai jiran gado Nayef bin Abdelaziz

Yawancin Alhazai na ziyartar Masallatai masu tsarki na Makka da na Madina inda aka binne Annabi Muhammad (SAW) ga shekaru fiye da dubu daya da 400 kenan. A yau din nan kuma Alhazai sun yi hawan Arfa, inda tarihi ya nuna cewa a can Annabi Muhammad (SAW) ya yi hudubarShi ta karshe a duniya.

Gobe Lahadi ake kammala aikin Haji da Eid al Adha ko Sallar Layya .

Aikin Haji na daga cikin shikashikai biyar na addinin Islama, wanda ya ke wajibi akan kowane Musulmi ko Musulma mai hali, sau daya a rayuwa.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG