Samson Siasia ya nemi da abashi iznin tafiya kasar Turkiyya domin domin kafa sansanin horas da ‘yan wasan sa, ya bukaci hakane a lokacin daya dawo gida Najeriya daga yawon shakatawa.
Shi dai Koch ne na ‘yan wasa ‘kasa da shekaru ashirin da uku (U-23) kuma yana shirye-shiryen karawa da kasar Gabon a wasan share fage da za’ayi a wata mai zuwa na Fabarairu a gasar cin kofin Afirka wato All Africa a turance, kuma a yanzu haka ya mika tsarin shirinsa zuwa ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF.
Siasia dai yace, “muna bukatar sansanin horaswa a gurin da ‘yan wasa bazasu shagala ba, kuma babu wani abu da zai dauke musu hankali, inda zasu fuskanta ga shirin da muka shirya domin samun horo na gaske batare da samun akasi ko matsala ba. Zan yi matukar godiya idan har hukumar kwallon kafar Najeriya, zata samar mana da sansanin da zamuyi horo akasar Turkiyya, a inda nake fatan zamuyi shiri na gaske batare da samun wani abu mai daukar hankali ba.”
Ya dai cigaba da cewa, “wannan zai zamo sauki ga ‘yan wasan dake waje da muka gayyato, ba wai sai sunyi tafiya har zuwa Abuja ba. Amma komai ya dogara ga shawarar da hukumar kwallon kafar Najeriya ta yanke.”
Your browser doesn’t support HTML5