Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Lamba Ta Daya: Arsenal Ta Lashe Kofin Farko Cikin Kwanaki 3,283


'Yan wasan Arsenal sun cira manajansu, Arsene Wenger, sama bayan da suka lashe kofin FA Cup a Wembley Stadium na London, Asabar, May 17, 2014. (AP Photo/Sang Tan)
'Yan wasan Arsenal sun cira manajansu, Arsene Wenger, sama bayan da suka lashe kofin FA Cup a Wembley Stadium na London, Asabar, May 17, 2014. (AP Photo/Sang Tan)

A lamba ta 1 cikin jerin abubuwan da suka fi girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014, a cewar editocin GOAL.COM, shi ne lashe kofin Kalubalenka, FA Cup, na Ingila, da kungiyar Arsenal ta yi.

Ba wai don ba ta taba lashe kofin ba ne, domin wannan shi ne karo na 11 da take yi, sai dai domin rabon da Arsenal ta lashe wani kofi, sai da ta shafe kwanaki dubu 3 da 283!!

Kuma a wasan karshe na lashe wannan kofin, da farko kamar Arsenal ba zata kai labara ba, domin kuwa Hull City ta zura mata kwallaye har biyu, na farko ma tun ‘yan kallo basu gama zama kan kujerunsu ba.

Da kyar Arsenal ta rama wadannan kwallaye biyu, kuma har aka cika lokaci a hakan, amma da aka yi Karin lokaci, ana dab da hura tashi sai Arsenal ta jefa kwalllo na uku, kuma sun a ci aka hura tashi.

A cewar editocin GOAL.COM, wannan kofin farko da Arsenal ta lashe cikin shekaru fiye da 9, kuma na farko tun lokacin da Arsene Wenger ya zamo manajanta, shi ne babban abinda ya girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014.

XS
SM
MD
LG