Tsohon dan wasan Chelsea Frank Lampard yayi alkawarin bazai yi murna ba idan har ya jefawa tsohon kulub dinsa kwallo a raga, a wansan daza suyi mai zuwa karshen watan nan.
Dan wasan tsakiyan dai ya bar kungiyar kwallon kafar yammacin ingila a kakar kwallo ta bara, inda yakoma kungiyar kwallon New Yorki City FC. Daga baya ya dawo Ingila, ya fara wasa da Manchester City.
A wannan satin ne, Premier League ta tabbatar da cewa bai taba sa hannu ko yarjejeniya da MLS ba. Abinda ya janyo kace-nace ga magoya bayan kungiyar kwallon Chelsea, kuma ana kyautata tsammanin wasu daga magoya bayan na iya masa ihu alokacin daya daya dawo domin buga wasa. Duk da haka ya dai tabbatar da cewa shi bai damu ba.
A lokacin da yake magana da gidan jaridar Times, yace, “Na rantse mahalarci, idan naje filin wasan sukayi mini ihu har na tsawon minti casa’in kuma na jefa kwallo a raga, bazanyi murna ba, kuma ban taba tunani a kwakwalwata ba cewar magoya baya zasu gane me nake ciki da yadda nake ji a zuciya taba, bazan taba murnar jefa kwallo ga ragar Chelsea ba.”