A lamba ta 2 cikin jerin abubuwa guda 10 da editocin GOAL.COM suka ce sune suka fi yin tasiri, ko suka fi girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014, akwai ci 7-1 da Jamus ta yi ma kasar Brazil, a gasar cin kofin duniya, kuma a kasar Brazil.
A tarihi dai, babu wanda ya taba doke kasar Brazsil da ci 7, sune suka saba yin hakan ma wasu kasashen.
Amma tun daga lokacin da zakaran dan wasan Brazil, Neymar, ya ji ciwo a wasannin kwata fainal, da alamun tamaular ta kubuce ma Brazil, har ya zuwa wannan wasan kusa da karshe da Jamus.
An dauka gasar cin kofin duniya ta 2014 zata kasance gasar Brazil, tunda a cikin kasarta ake yi, kuma ta yi shirin da aka dauka cewa zata lashe kofin.
Amma a karshenta, an ce ba a taba ba kasar Brazil kunya a filin kwallo kamar wannan ba. Haka aka ga ‘yan wasa da ‘yan kallo su na zabga kuka a bayan wasan.
Wane abu ne na daya a cikin abubuwan da suka girgiza duniyar kwallo a shekarar 2014? A biyo mu a shiri na gaba.