Sama Da Mutane 30, 000 Sun Rasa Matsugunansu A Derna, Libya - Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira

Derna, Libya

Ma'aikatan ceto na ci gaba da aiki yau Alhamis a gabashin Libya, inda wata mummunar ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, wasu dubbai kuma suka bata.

WASHINGTON, D. C. - Ya zuwa yanzu dai ba'a san iyakar yawan wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a kasar a ranar Lahadin da ta gabata ba. Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito Ministan lafiya na gabashin Libiya Othman Abduljaleel yana cewa an binne gawarwakin mutane 3,000 ana kuma ci gaba da shirya wasu 2,000.

Hassan El Salheen yana kuka bayan ya binne gawar ‘dansa

Abdel-Raham al-Ghaithi Magajin garin Derna, ya shaidawa gidan talabijin na al-Arabia cewa adadin wadanda suka mutu zai iya kaiwa 20,000.

Dena ita ce yankin bala’in ya fi shafuwa, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya da fashewar madatsun ruwa suka lalata gine-gine, da binne wurare a cikin laka da kuma gangara mutane zuwa cikin teku.

DERNA, LIBYA

Sakatare-janar na Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya Petteri Taalas, ya shaidawa manema labarai yau Alhamis a birnin Geneva cewa, "idan da kayan aikin nazarin yanayi na Libya suna aiki da watakila za'a iya samun saukin wannan masifar da yawan wadanda suka jikkata.

"Idan da suna da ofishin kula da yanayi da ya kasance mai aiki yau da kullum, da sun samu gargadi," in ji shi.

Derna, Libya

Aikin taimakon na kasa da kasa ya hada da tawagogi daga Masar da Aljeriya da Tunisiya da Turkiyya da Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa a jiya Laraba ta ce ambaliyar ruwa ta raba akalla mutane 30,000 a Derna da kuma wasu dubbai a wasu yankuna da matsugunansu.