Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Antonio Guterres yana kira ga kwamitin sulhu ya amince da kudurin tsagaita wuta na tsawon kwanaki talatin ba tare da bata lokaci ba a Syria domin a taimakawa kimanin mutane dubu dari hudu dake yankin Ghouta da ya ce “suna cikin matsanancin halin kunci”
Guterres ya ce, na hakikanta cewa, gabashin Ghouta ta gagara” ya ce “kirana ga dukan wadanda ke tashin hankalin shine su daina yaki ba tare da bata lokaci ba a gabashin Ghouta domin a iya kai kayan agaji ga mabukata.
Shekarar da ta gabata,aka ayyana yankin a matsayin daya daga cikin wuraren da za a daina tada hankali a wata yarejejeniya da aka cimma da magoya bayan Syria, Rasha da Iran da kuma Turkiya.
Sai dai an ci gaba da fada kwanan nan yayinda sojojin Syria da abokan kawancenta suka nuna alamar kaddamar da harin da nufin sake kwace yankin da ya kasance daya daga cikin yankunan da suka rage kusa da Damascus a hannun mayakan kungiyar hamayya.