Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Yi Watsi Da Tuhumar Katsalandan Da Amurka Ta Yi Ma Wasu Rashawa


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kamar yadda aka zata zai faru, kasar Rasha ta yi watsi da tuhumar da Amurka ke wa wasu 'yan kasarta su 13 da ta zarga da yin katsalandan a zaben kasar na 2016.

Kasar Rasha ta ce tuhumar da Amurka ta yi ma wasu ‘yan Rashar 13 da wasu kamfanonin Rasha uku bisa zargin cewa sun yi katsalandan a zaben Amurka na 2016 sokiburutsu ne kawai.

Da ya ke magana a wurin wani taro kan batun tsaro a Munich na kasar Jamus, inda dinbin Shugabannin kasashen duniya su ka taru a karshen wannan satin, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya jefa ayar tambaya kan sahihancin hujjojin da Ma’aikatar Shari’ar Amurka da kuma mai bincike na musamman Robert Mueller, su ka gabatar.

“Kun san ni ban da abin fadi ko muskalazaratin, saboda mutum na iya wallafa duk abin da ya ga dama. Ai mun ga yadda zargi, da kalamai da kazafi ke yado. Muddun ba mu ga shaida ba, duk wani abin da ake cewa shirme ne kawai. Don Allah a mani azuri saboda rashin amfani da lafazi irin na diflomasiyya.” In ji Lavrov.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG