Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Isra'ila Sun Bukaci Da A Gurfanar Da Firayim Minista Netanyahu Gaban Kotu


'Yan sanda a Isra'ila, sun bayar da shawarar cewa a gurfanar da firayim minista Benjamin Netanyahu a gaban kotu bisa zargin zarmiya da cin hanci a wasu laifuffuka biyu da aka bi8ncika.

Jiya talata hukumar 'yan sandan ta bani Isra'ila ta bayar da wannan shawara a bayan da ta shafe watanni tana binciken zargin cewa Netanyahu yana karbar kyautar kayayyaki masu tsada daga hannun attajirai. Har ila yau an yi zargin cewa yayi alkawarin taimakawa wani mai wallafa jarida idan har zai yarda yana buga labarai masu dadi a kansa.

Jim kadan a bayan da 'yan sandan suka gabatar da wannan shawara, Netanyahu ya fito a cikin telebijin na Isra'ila, yana cewa "Zan ci gaba da jagorancin kasar Isra'ila tsakani da Allah muddin ku al'ummar wannan kasa kun zabe ni da in yi hakan."

Ya kara da cewa wannan shawara ta 'yan sanda cewa a gurfanar da shi gaban kotu, "haka zata kare a banza."

Ana zargin Netanyahu da laifin karbar kyaututtuka, ciki har da wata irin taba mai tsada da ake kira Cigar, da wata barasa mai tsada ta alfarma, da kuma kayayyaki dangin sarka da agogo, daga hannun wasu manyan attajirai cikinsu har da wani Fardusa na Hollywood haifaffen Isra'ila, Arnon Milchan, da wani hamshakin mai kafofin yada labarai na Australiya, James Packer.

dadadden abokin adawar Netanyahu, tsohon firayim minista Ehud Barak, ya bayyana wannan zargin zarmiya da cewa mai tayar da hankali ne, amma Netanyahu yace wannan duk bi-ta-da-kulli ne 'yan sanda da kafofin yada labarai ke yi masa.

Yanzu ya rage ga atoni janar na Isra'ila, Avichai Mandelblit, ya tsayar da shawara a kan ko za a tuhumi Netanyahu da aikata wadannan laifuffuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG