Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Ki Karban 'Yan kasarta Da Aka Kama Suna Fada a Yakin Syria


Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron

Faransa ta ce sam ba za ta amince ta karbi mayakan jihadi da aka kama a fagen yaki a kasashen wajen ba wadanda asalin 'yan kasarta ne, da nufin ta hukunta su.

Jami’an Faransa sun yi kememe, sun ce ba za su karbi mayakan jihadin kasarsu da aka kama a fagen yaki a Syria da Iraqi ba, da nufin a masu shari’a a Faransan.

Bayan da aka kwashe kusan mako guda ana tattaunawa tsakanin kasashen yammaci kan makomar mayakan kasashen waje da ake tsare da su, Amurka ta nemi a mika su ga kasashensu na asali da suka fito.

Amma Faransa da Birtaniya sun ce sam ba za ta sabu ba.

Wani jami’in diplomasiyan Faransa da ya gana da Muryar Amurka, ya ce ko kusa da cimma matsaya ba a yi ba dangane da hakan.

Jami’in diplomasiyan ya kara da cewa, Faransa na gudun cewa mayakan da aka kama, za su yi amfani da kotuna wajen yada farfaganda da kuma kalubalantar adalcin da za ta yi musu.

Sannan da za ran an saka su a gidan yari, akwai yiwuwar su gurbata tunanin fursunonin da ke ciki.

Jami’in ya kara da cewa akwai sarkakiya a tsarin dokar Faransa, idan har aka ce za a hukunta mayakan a kasar, wadanda suka aikata laifuka a kasashen waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG