A yau ne aka soma shara’ar wata yarinya ‘yar Palesdinu wacce farmakin da ta kaiwa wasu sojojin Isra’ila guda biyu ya watsu ko ina a duniya, sai dai kuma alkalin kotun sojan dake sauraren shara’ar ya bada umurnin a gudanarda shara’a a boye.
Matashiyar mai suna Ahed Tamimi wacce a cikin watan jiya, yayinda take tsare a kurkuku ta cika shekaru 17 da haihuwarta, ta bayyana a kotun cike da annashuwa da nuna shirinta na fuskantar masu zargin nata, kuma kotun ta cika makil da ‘yan jaridu da jami’an diplomasiyar kasashe daban-daban.
Bayan lauyoyin dake gabatarda karar sun kammala karanta zarge-zarge 12 da ake mata ne, aka dage shara’ar har zuwa watan gobe.
Tun cikin watan Disambar bara ne dai aka kama wannan matashiyar bayanda aka ga hoton bidiyonta dake nuna inda take shurin wani sojan Isra’ila, yayinda take marin na biyu a gaban gidanta dake Yammacin Kogin Jordan.
Facebook Forum