A wani mataki na inganta huldar diflomasiyya da tattalin arziki da tsaro tsakanin Amurka da Afirka, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, zai kai ziyara Afirka daga ranar 6 zuwa 13 ga wannan wata na Maris.
WASHINGTON D.C. —
Shirin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson na kai ziyara Afirka, wata dama ce ta jaddada matsayin Amurka na mai taka muhimmiyar rawa wajen karfafa gwiwar nahiyar, da kuma jaddada muhimmancin cudanya, a cewar wani babban jami'in gwamnatin Amurka.
“Ba kawai kan batun bunkasa tattalin arziki da cinakayya ba, amma har ma da batun girke mashahuran madahun cigaba, da tsarin shugabanci da tsaro da kuma ‘yancin dana dam,” a cewar jami’in yayin hira da ‘yan jarida jiya Jumma’a.
Yayin da ya kai ziyara a Afirka, Tillerson zai gana da Shugabannin kasashen Chadi da Djibouti da Habasha da Kenya da kuma Najeriya, duk a yayin wannan zaiyarar da zai fara daga ran 6 zuwa 13 watan nan na Maris.