Sakataren ma’aikatar harkokin tsaron Amurka Jim Mattis ya gana da takwaransa na kasar Japan yau Juma’a a Tokyo, don a lafar da damuwar da KTA ta ke da shi akan sadaukarwar Amurka ga yankin, a yayin da ake neman kawo matsaya a yarjejeniyar dakatar da shirin Nukiliyar KTA.
Yau Juma’a, Mattis da ya tsaya kafa-da-kafada da Ministan tsaron Japan Itsunori Onodera, ya ce, "dangantakar Japan da Amurka na nan daram, duk da cewa muna tsaka-tsakiyar yarjejeniya tsakaninmu da KTA," inji shi
Ministan tsaron Japan Ondera, a nasa bangaren yace, Amurka ta amince zata ci gaba da atisayen sojoji tare da Japanawa. A farkon watan nan ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya bayana dakatar da atisayin sojin bayan ganawarsa da shugaban KTA Kim Jong Un.
Inda Shugaban yace, atisayin yana da tsada kuma yana haifar da tsokana a tsakani. KTA ta dade tana kiran a dakatar da wannan atisayin sojojin don tsoron yiwuwar kai mata hari, abinda sojojin Amurka da KTK suka musunta a baya.