Yara fiye da 10,000 ne aka kashe ko aka nakasa bara a tashe-tashen hankula a duk fadin duniya, a cewar wani rahoto na MDD.
An samu rahotannin mummunan cin zarafin yara har sau 21,000 a 2017, wanda ya nuna karuwar al'amarin sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, a cewar sakamakon binciken sashin nazarin tashe-tashen hankula da makomar yara.
"Yara kanana - maza da mata - sun kadu sosai da tashe-tashen hankulan da aka dade ana yi da kuma sabbi. Duk kuwa da cigaban da aka dan samu, har yanzu irin cin zarafin yara da ake yi ba abin yadda ba ne," a cewar wani mai magana da yawun Sakatare-Janr na MDD Antonio Gueterres a wata takardar bayani.
Rahoton ya tabo kasashe 20, ciki har da wuraren da al'amarin ya fi tsanani kamar su Yemen, da Siriya da kuma Afghanistan.
Facebook Forum