Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD da Kasashen Afirka Na Maraba da Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Sudan ta Kudu


Shugaban Sudan Omar Al-Bashir ya rike hannun shugaban Uganda Yoweri Museveni Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugn 'yan tawaye Riek Machar, bayan sun tabataba kan yarjejeniyar
Shugaban Sudan Omar Al-Bashir ya rike hannun shugaban Uganda Yoweri Museveni Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugn 'yan tawaye Riek Machar, bayan sun tabataba kan yarjejeniyar

Yarjejeniyar da shugaban Sudan ta Kudu da madugun 'yan tawaye suka rabtabawa hannu a kasar Sudan cikin wannan makon ya farantawa kasashen Afirka rai tare da samun karbuwa a Majalisar Dinkin Duniya

Kasashen Afirka a Kwamitin Sulhun MDD, jiya Alhamis sun yi maraba da rattaba hannu na dindindin da aka yi tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu da tsohon Mataimakinsa, to amma sun bayyana damuwar cewa, kamar sauran yarjajjeniyoyi na baya, wannan ma ba za ta dore ba.

Shugaba Salva Kiir da mai ja da shi kuma tsohon Mataimakinsa, Riek Machar, sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar ranar Talata a Khartoum.

Jakadan Sudan Ta Kudu a MDD, Akuei Bona Malwa, ya ce wannan yarjajjeniyar ta hada da sauran bangarorin da ke taka rawa a wannan tashin hankalin, kuma dukkanninsu sun yi alkawarin hada kai wajen maido da zaman lafiya a kasar.

Jakadan Habasha Tekeda Alemu ya ce kwanakin da ke tafe za su kasance da matukar muhimmnaci.

Ya kara da cewa:

"Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne, kamar yadda aka sani, dukkannin bangarorin su mutunta alkawarin da su ka yi su aiwatar da zaman lafiya."

Shi ma jami'in diflomasiyyar kasar Ivory Cost ya yi kira ga dukkannin bangarorin da su mutunta alkawarin da su ka yi, ya kuma ce gwamnatin kasarsa ta amince da girke sojojin hadin gwiwa na kungiyar kasashen Kuryar Afirka, domin tabbatar ana mutunta ka’idodin yarjejeniyar tsagaita bude wutar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG