Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada yau Laraba cewa gwamnatin kasarsa ta sha samun tambayoyi dangane da matakai marasa kan-gado kuma cike da rudani da sabuwar gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump take dauka.
Lavrov yana maganar ne a wajen taron da suka fara da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a Moscow, ya kara da cewa akwai bukatar Rasha ta fahimci manufar Amurka.
Lavrov kuma ya ambaci farmakin da Amurka ta kai Siriyya a makon da ya gabata, wanda maida murtani ne ga harin gubar da aka kai a Siriyya din, ya bayyana murtanin da Amurka ta maida a matsayin “abun damuwa”.
Tillerson bai yi wata doguwar magana a nasa jawabin ba, amma kamar Lavrov, shima ya ce ganawar ta yau Laraba na zuwane a lokaci mai muhimmanci kuma zata basu damar yin cikakkiyar tattaunawa akan bambamnce-bambancensu da kuma muradansu.