Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Zargi Korea Ta Arewa Da Neman Tsokana


Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump ya fada cewa Koriya ta Arewa na “neman rigima” muddin ta ce za ta ci gaba da kokarinta na kera makaman nukiliya, har ma ya kara da yin kira ga China da ta tsawata mata ganin cewa kawarta ce.

A cikin kalaman da ya rubuta akan shafinsa na Twitter, Trump ya ce “zai yi kyau idan China ta taimaka mana wajen shawo kan wannan matsalar, in kuma ba ta yi ba, mu za mu magance matsalar da kanmu.”

Sai dai Trump bai fayyace irin matakan da Amurkan za ta dauka wajen warware matsalar ta Korea ta Arewa ba.

Haka kuma ya ce ya shaida wa shugaban China, Xi Jinping a taron kolin da suka yi a cikin makon jiya cewa China za ta fi samun damar cin moriyar yarjeniyoyin cinikayyar da take neman kullawa da Amurka idan China din ta taimaka wajen “warware wannan matsalar ta.”

China dai ita ce babbar kasar da Korea ta Arewa ta dogara akanta fiye da kowace kasa a duniya, abin da ya sa har Cibiyar Nazarin Harkokin Waje ta Duniya take bayyana China a matsayin kasar da Koriya din ta dogara akanta wajen samun ci gaba a harkokinta na kasuwanci da makamai da abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG